An yi mata kwalliya.
    An yi mata damara.

    'Yan matan da ake turawa cikin mutane domin su tarwatsa kansu.

    News imageNews imageNews image

    Ana yi wa Falmata cikakkiyar kwalliya - an yi wa kafarta lallen fulawa mai ban sha'awa.

    Yayin da lallen ke bushewa, wata mata tana fama da gyara mata gashin kanta.Tana amfani da mataji wajen taje wa Falmata gashin kanta da ke a nannade.

    “An ba mu damar zaban salon da muke so dangane da kitson da lallen,” in ji Falmata yayin da take tuna yadda lamarin yake a baya. “Mu kan yi lallen a hannayenmu da kafafu da kuma wuya a wasu lokutan.”

    Falmata ta san za ta yi kyau, amma hakan na tattare da tasiri na mutuwa.

    Da zarar an gama mata kwalliya, za a daura mata damarar bam don yin kunar bakin wake.

    Falmata daya ce daga cikin daruruwan 'yan mata, wadanda yawancinsu ba su kai shekara 20 ba, kuma masu tayar da kayar baya suka sace a Najeriya suka kuma tilasta musu kai hare-hare.

    Abin mamakin dai shi ne ta tsira.

    'Yar shekara 13 ce da mutane biyu da ke kan babur suka sace ta yayin da take kan hanyarta ta zuwa gidan wasu 'yan uwanta kusa da bakin iyakar Najeriya da Kamaru.

    Sun shafe sa'o'i a kan babur - Falmata a makale tsakanin mazajen biyu - inda suka bar kan hanya kuma suka kutsa cikin wani daji.

    Daga baya, sun isa inda za su je - wani babban sansani na wucin gadi. Falmata ba ta san inda ta ke ba.

    “Akwai tanti da yawa da kuma gidajen zana masu yawa,” in ji ta, ta fada kamar tana rada.

    “An saka 'yan matan cikin tanti-tanti. 'Yan mata tara ne a cikin tantin da nake kuma ya zama mana dole mu kwanta kan manya-manyan tabarmai.”

    Sansanin na 'yan Boko Haram ne, kungiyar mayakan da take yakin neman kafa daular Musulunci a arewacin Najeriya.

    Ta ce: “Daga farko na so in arce amma babu dama.” An a ajiye maza a kewayen sansanin domin kama duk wanda ya yi kokarin guduwa.

    Sai dai kuma ba a jima ba kafin a tilasta wa Falmata ta zabi daya daga cikin biyu - ta auri wani mayaki, ko kuma ta je "aiki".

    Ta ki yin aure. “Na shaida musu cewa ban kai aure ba,” in ji ta.

    Amma ba ta san me suke nufi da "aiki" ba.

    ‘Aikin’

    News image

    Daga farko dai Falmata tana jin tsoro a sansanin.

    Yanayin rayuwar wurin na da wuya , kuma mutanen da aka kama - mata da 'yan mata da kuma yara - suna tsoron yaki tsakanin dakarun gwamnati da mayakan kungiyar masu tayar da kayar bayan.

    “Muna jin tsoron cewar sojoji za su far wa sansanin a ko wanne lokaci, kuma ba za su kyale mu, mata ba, domin za su zaci mu ne matan mayakan,” in ji Falmata.

    Idan jirgi mai saukar ungulu ko kuma wani jirgi ya bayyana a sama, hankulan mutanen da aka kama za su tashi, suna masu tsoron dakarun Najeriya za su jefa bam a sansanin.

    “Da muka gan su da yawa daga cikinmu sun yi kuka,” in ji ta. “Wasu daga cikinmu ma sun bata jikinsu da datti.”

    Rayuwa a sansanin ka iya kasancewa wata aba mai matukar gimsa.

    A tashi a yi sallah, a ci abinci, a yi wanke-wanke, a yi sallah, a ci abinci a kuma yi wanke-wanke - aikin kenan daga safiya zuwa dare.

    A ko wacce rana akwai lokacin karatun addini, sa'o'i masu tsawo na karanta ayoyi daga Kur'ani.

    Falmata ta ce duk da cewa ta tsani komai a sansanin, ta yi marhabin da koyarwar addinin.

    Wata rana, an katse wannan zama da ya addabi rayuwarta ta yau da kullum.

    Wasu mutane dauke da makamai sun ce wa Falmata ta shirya domin wani abu mai muhimmanci.

    Za a yi mata lalle a hannaye kuma za a tsefe mata gashin kanta.

    Shin ana mata shirin aure ne, ta yi tambaya a zuciyarta. Shin za a aurar da ita ga wani mayaki ne?

    “Kawata Hauwa ta yarda a yi mata aure domin tsira da rayuwarta,” in ji Falmata. “Tana son ta sami hanyar kubucewa.

    “Sauran 'yan matan sun tsane ta domin auren da ta yi. Kuma ni ma na tsane ta daga farko. Amma na fahimce ta kuma na ji tausayinta domin ba ta jin dadi."

    Matan sun taimaka wajen shirya Falmata.

    “Abin da nake tunani kawai shi ne 'wannan shirin na aure ne ko na me?' Amma ba za ki iya tambayar me yasa ake miki wannan shirin ba. Maimakon haka kawaye za su rarrashe ki kuma su gaya miki ki yi hakuri.”

    Bayan kwana biyu, sai mayaka suka yi mata kunzugu da bama-bamai.

    News image

    Mayakan sun shaida wa Falmata cewa idan ta kashe wadanda ba su yi imani ba za ta shiga Aljanna kai-tsaye.

    Kamar sauran matan, za ta yi hakon kasuwa ko kuma inda mutane ke da yawa.

    “Na ji tsoro sosai har na fara kuka. Amma sun ci gaba da gaya mini in yi hakuri, in yarda cewa makasudin rayuwa kenan," in ji ta.

    “Cewa idan na isa Aljanna komai zai kara kyau .”

    An dauke ta da sauran 'yan mata biyu- wadanda su ma an yi musu damara da bama-bamai- an kai su wajen wani kauyen da ba su gane ba.

    Sun rike kananan ababen tayar da bam da aka yi a gida.

    An bai wa 'ya matan umarnin zuwa wani kauye. An gaya musu wasu za su yi ta kallonsu daga nesa.

    A kan hanyarsu 'yan matan uku sun tattauna kan ko su aiwatar da "aikin" ko kuma kar su aikata.

    Shin za su yi yadda aka ba su umarni ne ko kuma za su arce ne?

    Sun yanke shawarar kada su kaddamar da harin.

    Bayan ta nemi wani bako ya taimaka ya cire mata damarar bam din, sai Falmata ta bi wata hanya mai kura.

    Jim kadan, ta hadu da wasu mutane biyu a gefen hanya.

    Ba ta gane da wuri cewa 'yan Boko Haram ba ne.

    An sace Falmata a karo na biyu.

    News image
    News image

    Tarihi mai cike da tashin hankali

    News image

    Ana tunanin Sanaa Mehaydali ita ce mace ta farko da ta fara kai harin kunar bakin wake a tarihin yanzu.

    'Yar shekara 16 din ta kashe kanta da sojojin Isra'ila biyu a wani harin kunar bakin wake a kudancin Lebanon a shekarar 1986.

    Tun wannan lokacin kungiyoyi irin su Hezbollah da PKK na Kurdawa da Tamil Tigers a Sri Lanka da Hamas da Black Widows a Chechnya duka sun yi amfani da mata wajen kaddamar da hare-hare kunar bakin wake.

    Amma Boko Haram dai ta dara ko wacce kungiya a matakin aikinta na rashin tausayi in ji Elizabeth Pearson, wata mai bincike a Royal United Service Institute a Landan.

    Ta yi kiyasin cewa an tilasta wa daruruwan 'yan mata kai hare-hare cikin shekaru uku da suka wuce a Najeriya da kamaru da Chadi da Kuma Nijar.

    A karshen shekarar 2017 mata da 'yan mata 454 da aka tura harin kunar bakin wake sun shiga hannu a wurare 232, in ji Pearson. Hare-haren sun kashe mutum 1,225.

    Pearson ita ce ta wallafa wani bincike game da yadda Boko Haram take amfani da mata a matsayin 'yan kunar bakin wake.

    Kungiyar ta fara tilasta wa 'ya mace kai hari ne a watan Yunin shekarar 2014.

    An tayar da bam a wani barikin 'yan sanda jim kadan bayan an sace 'yan makarantar sakandaren 'yan mata ta Chibok 276.

    Boko Haram ta sace 'yan mata da ma manyan mata kafin wannan lokacin kuma sace-sacen ba su ja hankalin duniya ba, amma na 'yan matan Chibok ya fita daban.

    Sace 'yan matan daga dakinsu na makaranta a jihar Borno ya janyo Allah-wadai daga fadin duniya.

    “An kara saninsu kan wannan harin fiye da yadda aka ji su kan amfani da yara maza wajen kaddamar da hare-haren kunar bakin wake. Shi ya sa suka ci gaba da amafani da 'yan mata," in ji Pearson.

    Fatima Akilu masaniya ce kan halayyar dan Adam kuma ita ce daraktar gidauniyar Neem Foundation, da ke tallafa wa al'ummomin da yakin Boko Haram ya rutsa da su.
    Ta yi aiki da mata da kuma 'yan matan da aka 'yanta.

    Ta ce da farko samari ne suke kai hare-haren kunar bakin wake - irin wadanda akidar Boko Haram da kalamanta suka rinjaya.

    Ta ce: "Yawancinsu suna kai hare-haren kunar bakin waken ne da radin kansu domin sun yi imanin cewa za su wuce Aljanna ne kai-tsaye."

    Ta kara da cewar: " A lokacin da hare-haren sojin Najeriya suka kara tsanani, yawan matasan da suke fitowa kai hare-haren kunar bakin wake domin radin kansu ya ragu sosai. Saboda haka sai Boko Haram ta fara satar 'yan mata kuma tana tilasta musu kai hare-haren kunar bakin wake.

    “Suna haka ne domin su iya kai hari ko ta yaya domin su ci gaba da wannan zub da jinin, wannan abin tsoron."

    Kuma da alama ba sa duba karancin shekaru a wannan lamari na rashin tausayin.
    A watan Disambar shekarar 2016 an yi amfani da wasu yara mata biyu da aka ce wadanda shekarunsu ba su wuce bakwai zuwa takwas ba wajen kai harin kunar bakin wake a wata kasuwar da ke arewa maso gabashin Najeriya. A wannan harin an kashe mutum daya kuma an jikkata 17.

    Tserewa

    News image

    Bayan an sake sace ta a karo na biyu, an kai Falmata cikin daji. Amma wani sansani na daban aka kai ta a wannan karon.

    Wadanda suka kama ta 'yan wani reshen Boko Haram na daban ne kuma ba su san cewa a wancan lokacin ba ta dade da fatali da harin kunar bakin wake ba. Da sun sani, mai yiwuwa ne su kashe ta.

    Rayuwa a wannan sansanin kamar rayuwar sansanin farko ne.

    Irin rayuwa ce ta ci da wanke-wanke da sallah da karatun addini kuma barci.

    Gidauniyar Neem Foundation ta ce sau da yawa mata da yaran da aka kubutar daga hannun 'yan Boko Haram su kan rungumi akidar kungiyar.

    Dr Akilu ta ce: " Yawancin wadanda muka hadu da su wadanda suka kasance a cikin wadannan sansanonin ba su da cikakken ilimi na boko ko na islamiyya.

    “Da yawa daga cikin su sun fara koyon karatun Al-kur'ani ne a lokacin da suka shiga hannun Boko Haram.

    “Suna rike da daruruwan mutane a sansanoninsu, kuma babu wani abun da zai debe musu kewa a kullum. Saboda haka su kan shafe sa'o'i hudu zuwa biyar na karatun addini. Mutanen da ke da hannu sai su yi amfani da addini a matsayin wani abin debe kewa.

    Bayan kimanin wata daya a cikin sabon sansanin, an sake bai wa Falmata zabi biyu- aure ko aiki.

    Ta sake kin aure. Amma a wannan karon ta yi wayo da aka zo fagen 'aiki'.

    An yi mata lalle kuma aka ba ta tufafi mai kyau. An daure mata damarar abubuwan fashewa a ciki kuma an rufe ta da doguwar riga da dan kwali.

    Amma a wannan karon ta tsere cikin daji jim kadan bayan da mayakan suka bar ta.

    Ta ce: “Na hadu da wasu manoma kuma na nemi su taimaka mini wajen cire damarar bam din. Na shaida musu cewan an tilasta mini kaddamar da harin ne, amma ba na son in kaddamar da shi.”

    “Sun ji tsoro amma sun ji tausayi na kuma sun cire shi.

    Ta yiwu sun yi tunanin cewa in sun ki zan iya tayar da bam din in kashe mu gaba daya
    News image

    Falmata ta bar manoman kuma ta shafe kwanaki a cikin dajin tana neman hanyar komawa Maiduguri, da kuma komawa ga 'yan uwanta.

    A kan hanya ta shiga cikin wasu mafarauta wadanda suka ba ta damar tafiya tare da su.

    Amma mayakan Boko Haram sun far wa mafarautan. Cikin hatsaniyar da aka shiga, Falmata ta sulale cikin daji.

    "Ban san dajin ba. Duk wani motsin da na ji na ba ni tsoro. Saboda haka, na ci gaba da tafiya. Na kan kwana a kan bishiya idan zan iya, " in ji ta.

    “Ina ganin na shafe mako daya ba tare da cin abinci ba. Na kan sha duk wani ruwa da na samu ko ada wanda ba ya gudana ne tare da wanke hannaye da kafafuna da shi a lokacin da zan yi sallah.

    “Nakan yi sallah sau biyu ko uku a yini a duk lokacin da na sami ruwa . Na tsorata sosai, amma Allah ya taimaka mini kuma na kai ga wani gari."

    Iyalan wani gida sun taimaka mata da wurin kwanciya na 'yan kwanaki, kana suka sada ta da danginta a Maiduguri.

    “Falmata ta shafe watanni bayan ta tsere tana a boye . Tana tsoron cewa hukumomi za su gane ta , kuma za a kama ta.

    'Yan mata kamarta suna bukatar lokaci domin su kara karfafa dankon zumunci da 'yan uwansu, in ji Dr Akilu.

    "Ta dade da barin 'yan uwanta kuma mai yiwuwa ne ta sauya a wannan lokacin. Amma zai iya yiwuwa 'yan uwanta su ma sun sauya kuma su kasance suna da nasu bacin ran."

    Kamar iyalai da dama a arewa maso gabashin Najeriya, yakin ya daidaita iyalan Falmata.

    A halin yanzu tana zama ne da mahaifiyarta a wani sansanin 'yan gudun hijira. Suna cikin wani mawuyacin hali, amma babu wanda ya san labarinta.

    Mummunan martani

    News image

    A lokacin da suka samu suka fice a raye daga sansanonin Boko Haram, samun irin wannnan damar na da wuya, 'yan mata irin su Falmata su kan fuskanci babbar matsala.

    Jami'an tsaro su kan kama yawancin wadanda ba su tayar da bama-bamansu ba inda suke kai su "cibiyar raba masu tsattsauran ra'ayi da akidarsu."

    Sojoji ne suke jan ragamar wadannan cibiyoyin kuma ba a san abin da ke faruwa a cikinsu ba.

    A tsakiyar watan Janairu, rundunar sojin ta ce sake rukuni na farko daga cikin mutanen da ta raba da tsattsaurar akida, amma babu tabbacin inda suke a halin yanzu.

    'Yan kadan da ba su samu sun sulale cikin jama'arsu ba tare da an sani ba, suna buya ne.

    Mutane suna kiran wasu daga cikin wadanda suka tsere daga sansanonin "annoba."

    Dr Akilu ta ce duk wata yarinyar da ta zauna da masu tayar da kayar bayan, mutane da dama suna yi mata kallon 'yar Boko Haram.

    “Ina ganin mutane a cikin wadannan garuruwan suna kallon aikin ne, maimakon kallon yarinyar.

    “In suka ga yarinya, sai su yi tunanin wannan wata ce wadda za ta iya kashe al'umma, ta ya ya za mu karbe ta?"

    Ta ce 'yan matan suna tuna musu irin ukubar da suka sha.

    Ana yi wa Boko Haram kallon daya daga cikin kungiyoyin masu tayar da kayar baya da suka fi kisa a tarihin zamani. Tun shekarar 2009 sun kashe sama da mutum 27,000, ciki har da Musulmai - a cikin Najeriya kadai.

    An kashe karin mutane masu yawa a Kamaru da Chadi da Nijar. Yakin ya raba fiye da mutum miliyan biyu da muhallansu.

    "Boko Haram ya shafi Kusan kashi 90 cikin 100 na al'ummomin arewa maso gabashin Najeriya. Sun rasa ko 'yan uwa ko kuma sun rasa iyalai gaba daya," in ji Dr Akilu.

    “Saboda haka a lokacin da 'yan matan suka dawo sai ciwon ya zama sabo. Akwai babbar matsalar nuna wariya.

    “Ba ma bayar da isasshen lokaci domin ganin lamarin ta yadda 'yan matan suke gani, kuma a gansu a matsayin wadanda abun ya shafa."

    News image

    A karo na biyu da aka yi wa Falmata damara da bama-baman kunar bakin wake tana 'yar shekara 14 ne.

    Ta shafe sama da shekara daya ba ta ga 'yan uwanta ba.
    An kulle ta a sansanonin masu tsattsaurar ra'ayi kuma aka cusa mata tsauraran akidun addini.

    Ta dandana 'yanci, amma wannan bai dade ba.

    Toh, me ya sa ba ta tayar da damarar kunar bakin wakenta ba komai ya kare a lokaci daya?

    “Na so in rayu," in ji ta.

    "Kisa ba shi da kyau. Abin da aka koya mini kenan a gida, kuma abin da ni ma na yi imani da shi kenan."

    News image