Dan jaridar Freedom na fuskantar barazana
Kwamitin kare hakkin 'yan Jarida a Najeriya ya baiyana damuwa da barazanar da wasu mutane suka yi wa wani dan Jarida na gidan rediyon Freedom a Kano Nasiru Salisu Zango game da labarin da ya wallafa na zargin lalata yara a wata makaranta mai zaman kanta a Kano.
Abdullahi Tanko Bala ya tattauna da Nasiru Salisu Zangon game da barazanar da ake yi wa rayuwarsa ga kuma karin bayanin da ya yi masa.