Ebola: Ana sa ran fitar da hanyoyin magance ta

Ebola ta kashe mutane kusan 2000 a yammacin Afirka

Asalin hoton, afp

Bayanan hoto, Ebola ta kashe mutane kusan 2000 a yammacin Afirka

Hukumar Lafiya ta Duniya WHO na saran fitar da wata shawara akan hanyar da za abi wajen magance cutar Ebola daga bisani a yau.

Sanarwar na zuwa ne bayan da kwararru 200 suka gana a Geneva, domin nazarin ingancin wasu hanyoyin magance cutar da ake gwajinsu guda Takwas, da kuma maiyiwuwa wasu alluran rigakafin kamuwa da kwayar cutar guda biyu.

Cutar ebola a Yammacin Afirka tayi sanadiyyar mutuwar mutane kusan dubu- biyu, kuma 400 daga cikinsu sun rasa rayukansu ne a makon daya gabata kadai