Uganda ta jinkirta dokar luwadi

Shugaba Museveni ya bukaci kwararru Amurkawa da su taimaka a binciken
Bayanan hoto, Shugaba Museveni ya bukaci kwararru Amurkawa da su taimaka a binciken

Shugaban Uganda, Yoweri Museveni, ya ce yana son ya jingine wani daftarin kudurin doka mai janyo kace-nace da ya shafi 'yan luwadi.

Zai yi hakan ne domin ya ba masana kimiyya damar gudanar da bincike a kan ko ana haihuwar mutum dan luwadi ne, ko kuwa sa kansa yake yi.

Tun farko, daftarin kudurin da aka gabatar a shekara ta 2009, ya tanadi hukuncin kisa ne a kan duk mai irin wannan halayya.

To amma daga baya sai aka yi masa gyaran fuska, inda aka soke hukuncin kisa a madadinsa aka sanya dauri a gidan yari ga wanda aka samu da laifin neman jinsi daya.

Shugaba Museveni ya ce, masana kimiyya na Uganda ne za su gudanar da binciken.

A cewar masu aiko da rahotanni, shugaban Ugandar yana tauna taura biyu ne - watau yana nema ne ya faranta ran masu zabe a kasar masu ra'ayin 'yan mazan jiya, sannan a daya bangaren ba ya son ya nuna wariya ga masu ba da agaji na kasashen turawa.