Shekara 50 da fafutukar Biafra

Wakilinmu Abdulsalam Ibrahim Ahmed ya dauko mana hotunan gangamin masu fafutukar neman kafa jamhoriyar Biafra

Shekara 50 da fafutukar Biafra
Bayanan hoto, A ranar 30 ga watan Mayun shekara 1967 masu fafutukar kafa Biafra suka ayyana ballewa daga Najeriya, har zuwa watan Janairu na shekarar 1970.
Shekara 50 da fafutukar Biafra
Bayanan hoto, Akasarin masu fafutukar 'yan kabilar Igbo ne da ke yankin kudu maso gabashin Najeriya.
Shekara 50 da fafutukar Biafra
Bayanan hoto, Wasu kananan kabilu da ke cikin masu fafutukar kafa jamhoriyar Biafra sun hada da Efik da Ibibio da Annang da Ejagham da Eket da Ibeno da Ijaw da sauran su.
Shekara 50 da fafutukar Biafra
Bayanan hoto, Masu fafutukar suna zargin cewa ana mayar da su saniyar ware a al'amuran tafiyar da Najeriya
Shekara 50 da fafutukar Biafra
Bayanan hoto, An sha samun tashe-tashen hankali sakamakon fafutukar ta masu neman kafa jamhuriyyar Biafra.
Shekara 50 da fafutukar Biafra
Bayanan hoto, Masu fafutukar sun kirkiro tuta da kudi na Biafra da suke burin amfani da su in hakkarsu ta cimma ruwa.
Shekara 50 da fafutukar Biafra
Bayanan hoto, A wasu wurare da suka hada da jihar Anambra, masu fafutukar sun yi artabu da jami'an tsaro yayin gangamin nasu.
Shekara 50 da fafutukar Biafra
Bayanan hoto, Rundunar 'yan sandan Najeriya ta bayar da umurnin a kwace makamai da ke hannun masu fafutukar Biafra.