Hotunan girgizar kasar Nepal

Shekara guda bayan mummunar girgizar kasar da ta yi sanadiyar mutuwar akalla mutane 9,000, mai daukar hoto, Gideon Mendel, ya fito da wasu hotuna da kuma labarai da ke nuna yadda taimako kadan ya ceci iyalai da dama da girgizar kasar ta rutsa da su.

Nepal. Gideon Mendel / Kungiyar agaji ta Christain
Bayanan hoto, Mai daukar hoto Gideon Mendel ya shafe tsawon rayuwar aikinsa yana tara bayanai a kan al'amuran yau da kullum a duniya. A baya bayan nan ya je Nepal domin kungiyar bayar da agaji ta Christain ta bayar da bayani a kan mutanen da al'amarin ya shafa sakamakon girigzar kasar da ta yi sanadiyar mutuwar mutane a kalla 9,000.
Laxmi Gurung. Gideon Mendel / Kungiyar agaji ta Christain
Bayanan hoto, Shekarar Laxmi Gurung 30 a duniya kuma ya mallaki wani dan karamin Otal a garin Baluwa da ke Gorkha, ta dafawa makwabtanta abincin da take kasuwancin da shi. " A lokacin da girgizar kasar ta auku, ta lalata dukkanin gidaje. Ta ce, "mun godewa Allah mun tsira daga mutuwa. Kowa yana jin yunwa. Ban bata lokaci wajen taimakawa mutane da abinci ba. Duk abin da na dafa, sai na rarraba kadan-kadan kowa ya samu."
Chandra Ghale. Gideon Mendel / Kungiyar agaji ta Christain
Bayanan hoto, Chandra Ghale, mai shekara 32, yana aikin gini kuma dan garin Baluwa da ke Gorkha ne, yana cikin tawagar bayar da agaji da aka kafa bayan girigizar kasar. Ya taimaka wajen hada kan al'ummar kuma ya raba kayan agaji a lokacin da aka kawo su. "Ina gida tare da yara na sai kawai muka ji kara kuma sai kasa ta fara girgiza. Bayan wani dan lokaci sai ginin ya rushe. Ba ma iya gani sosai saboda kura da kuma hayakin da ke fitowa daga baraguzan ginin.
Indra Kumari. Gideon Mendel / kungiyar agaji ta Christian
Bayanan hoto, Indra Kumari na tare da wani wanda zai sayi abu a shagon danginsu a lokacin da girigizar kasar ta fara. " Bayan girgizar kasar sai aka fara ruwan sama sai mutane suka zauna a karkashin rumfa. Kusan mu 35 ne mu ka zauna tare a ranar. Mun shiga wani hali na ha'ulai. Dangi na sun yanke shawarar bai wa kowa abinci daga shagon, taliyar indomie da shinkafa da mai da dankali da albasa da kwai da kuma hatsi. Ba a samu karancin abinci ba. A lokacin da aka yi kwana hudu da girgizar kasar, mun ciyar da mutane kusan 72."
lokbahadur Magar, Gideon Mendel / kungiyar agaji ta Christian
Bayanan hoto, Gidan Lokbahadur da ke Gorkha ya rushe kuma mutane 12 ne suka mutu a kauyen. "Kowa ya tsorata. Ana ruwa a lokacin kuma sai duk muka rikice. Rumfuna biyu ne ko uku iyalai 40 za su yi amfani da su kuma an ware wa mata da yara da tsofaffi ne. Bayan haka sai al'ummar suka fara tsara abubuwa da kansu. Wasu sun fara kawar da gawarwaki kuma su ka fara shirya jana'iza. Wasu kuma sun kwashe barguzai a wani yunkurin neman abinci. Na taimaka wajen bai wa wadanda su ka jikkata kulawa. Muna dafa abinci tare, mu ci tare kuma mun zauna tare. Sai da muka shafe kwananki uku kafin mu samu agaji.
Dhan Kumari Magar da Krisha Thapa tare da dan ta.
Bayanan hoto, Dhan Kumari Magar mai shekara 44, malamin makarantar firamare ne, ya taimaka wajen bai wa Krisha Thapa mai shekara 28 da jaririnta agaji. " Gidaje da dama sun rushe sosai kuma mutane sun makale a baraguzan ginin," inji dhan. " Na taimakawa wata mata da jaririyarta mai wata shida da haihuwa da ke wani gida da ke kusa. Sun makale ne a karkashin baraguzai kuma matar ta fita daga hayyacinta. Mun kwashe baraguzan ginin sannan mu ka fito da su, amma kuma ta yi fama da ciwon jiki bayan ta farka. Abin tausayi ne ganinsu a cikin baraguzan ginin nan."
Manoj Rana. Gideon Mendel / kungiyar agaji ta Christian
Bayanan hoto, Manoj Rana mai shekara 20 na Kathmandu a lokacin da girgizar kasar ta auku. Ya koma kauyen da ya girma. Ya ce " Rumfunan sunyi kaca-kaca kuma mutane sunyi yawa. Ya ce "Sai ya yi kama da wani abu na mutanen da. Dabobbi da dama sun mutu kuma su na ta wari. Sai na bai wa yara umarnin su kwashe mushe daga baraguzan su birnesu. Sai na samar wa al'ummar wurin dafa abinci. Kowa yana jin yunwa a lokacin. A tsawon wannan lokacin mun samu yawan abinci da za mu iya ci ne kawai sau daya a rana. Mun yi murna sosai a lokacinda mu ka samu agaji.
Sagar Tamang, Gideon Mendel / kungiyar bayar da agaji ta christian
Bayanan hoto, Kauyen Sagar Tamang ya lalace baki daya. Yana daga cikin wani karamin kwamiti da suka taimaka wajen samar da wani sansani na wucin gadi a wajen gari a Dhading ga al'ummar. " Da farko dai mun gina bandakuna saboda yana da muhimmanci ga tsaftar muhalli. Sai mu ka bukaci ruwan sha daga wurin hukumomi. An nada ni a matsayin shugaban kwamitinmu kuma mun nemi taimako daga wajen kungiyoyin bayar da agaji ta hanyar aike musu da wasiku. Mutanen gari kuma sun bamu tantuna da zanuwan gado. Wani bako da ya zo yankin ya bamu tantuna bakwai. Bayan wadannan abubuwan ne muke samun baci mai dadi."
Bal da Phul Sunar. Gideon Mendel / kungiyar agaji ta Christian.
Bayanan hoto, Bal da Phul Sunar 'yan garin Jyamrung ne da ke Dhading "kabilarmu 'yan tsiraru ne saboda haka ba mu zauna tare da sauran al'ummar ba. A maimakon hakan, sai mu ka kakkafa wurin da za mu zauna na dan lokaci a kusa da wani fili, inda mu ka yi amfani da abubuwa daga cikin gidajen da su ka rushe . Daga baya sai mu ka samu kwanunkan rufi daga wajen wani mai kudi. Ya bayar da kwanukan rufi ga duk wani dan Dalit da ke nan. Ya san dukanmu talakawa ne kuma ba mu da sana'a. Wani mai kudi a kauyen da ke makwabtaka ya ba mu shinkafa da mai da kuma gishiri, ya taimaka sosai a lokacin."
Ranjit Bishokarma da Rakesh Lamicchane. Gideon Mendel / kungiyar agaji ta Christian
Bayanan hoto, Rakesh Lamicchane, mai shekara 17, yana daya daga cikin mutanen da aka bai wa horon kai agaji kuma ya bayar da agaji da wuri a lokacinda aka yi girigizar kasa na biyu a 12 ga watan Mayu. Kungiyar Rakesh na matasa sun dauki tsawon mintuna 40 su ka kwashe baruguzan ginin kuma suka ceto Ranjit Bishokarma ( da ke hannun hagu a hoto) wace ta makale a karkashin baraguzai. Duka hotuna: Gideon Mendel / Kungiyar agaji na Aid.