Kayan da masu ciki ke zubawa cikin jakarsu

Masu daukar hoto sun leka cikin jakankunan masu ciki a sassa daban-daban na duniya don ganin me ke ciki.

Ellen
Bayanan hoto, Ellen 'yar kasar Malawi ta haihu a cibiyar lafiya ta Simulemba, inda ake haifar jarirai fiye da 90 cikin wata daya, amma kuma basu da tsaftataccen ruwan sha da kayan aiki tsaftatattu, kuma ban daki hudu ne kawai a cibiyar inda mutane 400 ke amfani da shi da kuma wajen wanka da babu kofa da rufin kwano.
Jakar kayan haihuwa ta Ellen
Bayanan hoto, A cikin jakarta kuwa babu komai sai tocilan da bakar ledar da za a shimfida a kan gadon haihuwa da reza ta yanike cibiyar jariri, da takardar 200 ta kudin Malawi wato kwacha, da kuma dogayen zannuwa uku da za ta dinga daurawa yayin zaman da za ta yi a cibiyar na tsawon makonni hudu da kuma wanda za a lullube jaririn da za ta haifa a ciki.
Deanna
Bayanan hoto, Deanna na zama a birnin New York. Wannan ce haihuwarta ta farko. Ta ce, "Ina matukar jin dadin kasancewa cikin wannan rayuwa ta goyon ciki, gaskiya wata mu'ujiza ce." kuma na yi sa'a gidana bashi da nisa da asibiti ma fi kyau a birnin New York. Samun ciki yana sa muna kara gane irin sa'ar da muka yi ta samunabubuwan da masu haihuwa ke bukata mafi inganci da kuma samun tsaftataccen ruwan sha. Kana son samarwa jaririnka abu mai kyau, amma akwai tashin hankali idan ka yi tunani cewa ba lallai ka samu tsaftataccen ruwan sha da ingantaccen asibiti ba. Da duniya za ta yi kyau in har dukkan mata suka samu tsaftataccen wajen da za su dinga haifar 'ya'yansu.
Jakar haihuwar Deanna Neiers
Bayanan hoto, A cikin jakarta ta shirin haihuwa kuwa akwai na'urar jin wake-wake da man tausa da wasu mayuka na shafawa a jiki da dan abin makulashe da rigar mama da audugar mata da bargo da kuma doguwar riga.
Takako Ishikawa kuwa 'yar Japan ce. Ta ce, "Lokacin da na yi haihuwata ta farko, abubuwan da na sanya a jakata su ne pampas da audugar gogewa yara najasa da kayan bacci. Amma wannan karon da yake wani asibitin ne daban da wancan, asibitin ne ke bayar da wadannan kayayyaki duk a cikin kudin da ka biya. Hakan yana da kyau saboda ba sai na damu kaina da tunanin yadda zan wanke kayana ba."
Bayanan hoto, Takako Ishikawa kuwa 'yar Japan ce. Ta ce, "Lokacin da na yi haihuwata ta farko, abubuwan da na sanya a jakata su ne pampas da audugar gogewa yara najasa da kayan bacci. Amma wannan karon da yake wani asibitin ne daban da wancan, asibitin ne ke bayar da wadannan kayayyaki duk a cikin kudin da ka biya. Hakan yana da kyau saboda ba sai na damu kaina da tunanin yadda zan wanke kayana ba."
Jakar haihuwar Takako
Bayanan hoto, A cikin jakar Takako ta haohuwa akwai katinta na inshora da fom dinta na asibiti da fom dinta na bayar da gudunmowar jini da littafinta na awo, da rigar mama da bulumboti da rigar masu ciki da man wanke kai da burushi da takardar goge bayan gida da kuma kayan jariri.
Hazel
Bayanan hoto, Hazel 'yar shekara 27 ta fito ne daga kauyen Hamakando a yankin Monz daga kasar Zambiya. Ta ce, "Akwai famfon tuka-tuka a asibitin amma babu ruwan famfo a bangaren masu haihuwa. Na sha jin tsoffin mata na cewa bai kamata mai ciki ta yi kaza ba ko kuma ga abin da ya kamata mai ciki ta yi. Daya daga cikin abubuwan da aka gaya min shi ne kar na yi bacci mai tsawo da rana. An ce min idan na yi haka, to jaririn ma zai yi bacci lokacin da aka zo haihuwarsa. An kuma ce ka da na dinga tsayawa a dokin kofa saboda idan na yi haka to a lokacin haihuwa jaririn zai tsaya a hanya ya ki fitowa da wuri. Sannan kuma an ce min na daina sakala dankwalina a wuya ko saka sarka lokacin da nake da ciki saboda cibiyar jaririn na iya nannade masa wuya."
Jakar haihuwar Hazel
Bayanan hoto, A cikin jakar Hazel kuwa akwai auduga da mazubin ruwa da ledar da za a shimfida a kan gadon haihuwa da bargon jariri da kuma rigar jariri.
Joanne
Bayanan hoto, Joanne mazauniyar London ce 'yar shekara 34, kuma tana da cikin fari. Ta ce, "na shirya gorar ruwana, 'yar uwata ta bani shawarar yin hakan ko da zan ji kishi a dakin haihuwa. Na yi tunanin ba sai na zuba ruwa a gorar tun daga gida ba sai na zo asibiti tukunna. Saboda na san ba yadda za a yi a rasa tsaftataccen ruwan sha a asibitin, ba kamar a Afrika ba. Abu ma fi muhimmanci a jakata shi ne bargon da mahaifiyata ta bani wanda zan lullube jaririna lokacin da zan koma gida, kuma wannan bargo shi ne wanda ni ma aka lullube ni lokacin ina jaririya."
Jakar Joanne Laurie
Bayanan hoto, A cikin jakarta akwai kayan ciye-ciye da yawa da kayan sawa da tawul da kayan wanka da audugar mata da da ipad da gorar ruwa da takardun asibiti da hankici da kayan jariri da kuma bargo.
Kemisa Hidaya
Bayanan hoto, Kemisa Hidaya matashiya ce mai shekara 27. Ta haihu a cibiyar lafiya ta Kawaala da ke Uganda, babban birnin Kampala, inda ba a cajar mutane kudi. A shirye-shiryen haihuwar da take yi, wata ungozoma ta bata jerin kayayyakin da za ta zo da su asibiti ranar haihuwa, wadanda suka hada da zanin gado da ledar da za a shimfida a gadon haihuwa da safar hannu guda 10. TA ce amma safar hannun biyu ta saya don bata da kudin sayen goma. Sai kuma reeza da audugar da za a goge jini da ita.
Jakar Kemisa Hidaya
Bayanan hoto, Kemisa ta kara da cewa, "Baya ga wadannan abubuwa da ungozoma ta bukaci na taho da su, akwai kuma wasu abubuwan da na saya musamman don jaririna, wadanda suka hada da zanin gadon jarirai da rigar sanyi da hula da kuma safa. Daga cikin wadannan kayayyaki wanda na fi so shi ne shawul din da za a sa jariri a ciki da kuma rigar sanyin saboda za su samarwa jaririna dumi. Yanzu kwanana daya da zuwa asibitin nan, kuma na gamus da tsaftar bandakin da bangaren haihuwar wanda ake tsaftace shi sau biyu a rana. Ina mamakin yadda zan iya haihuwa a wajen da ba isasshen ruwa, saboda a lokacin haihuwa ana zubar da jini sosai da ke bukatar a goge da gaggawa. Idan kuwa ba isasshen ruwa lokacin haihuwa, akwai yiwuwar jaririn da mai jegon duk su kamu da cuta."
Cathelijne Geuze
Bayanan hoto, Cathelijne Geuze 'yar kasar Netherland amma yanzu tana zama a Biritaniya. Ta ce, "Da kaina na hada abubuwan da na san zan bukata, jariri baya bukatar abubuwa da yawa lokacin haihuwarsa. Na san suna da komai a asibitin, amma gara ka tambaye su abin da ka ke so don su kawo maka da wuri. Abu ma fi muhimmanci a jakar shi ne bargon da Yakumbona ta saka min da kanta, mamana ce ta sayo zaren. Shi ne abu na farko da na fara hadawa a jakar."
Jakar haihuwar Catherine
Bayanan hoto, A cikin jakar haihuwar Catherine akwai kayan jariri da kayanta na sawa da nafkin da kayan kwalam da ipad da gorar ruwa da kuma kyamarar daukar hoto. Dukkan hotunan mallakin kungiyar agaji ne ta WaterAid - www.wateraid.org