Kantunan shan gahawa a Indiya

Wani mai daukar hoto Stuart Freedman ya yi tattaki zuwa Indiya inda ya zagaya wasu daga cikin shagunan shan shayi wadanda ake samun su a kowanne lungu da sako na kasar.

Hoton wani ma'aikacin shagon shan shayi da ke Kolkata, yana bai wa yara 'yan makaranta shayi, daga saman bango ana iya kallon zanen hoton Rabindranath Tagore.
Bayanan hoto, Stuart Freedman yayi wa wannan tafiya lakabi da "The Palaces of Memory." Ya kuma gano cewa masu shagunan shan shayi suna da kungiya.
Hoton shagon shan shayi na Shimla a Indiya.
Bayanan hoto, A cikin shekarun 1950 ne aka kungiyar masu shagunan shan shayi ta yadu a cikin kasar.
Mista Sri Kumar wani mai'aikaci a shagon sayar da shayi a Jaipur.
Bayanan hoto, A dalilin wannan aiki dai Mista Freedman ya ziyarci fiye da fitattun shagunan shan shayi 30 a biranen Indiya. Wannan hoton Sri Kumar ne wani mai'aikaci a shagon sayar da shayi a Jaipur.
Abokan ciniki zaune kusa da inda aka makala hoton Rabindranath Tagore a shagon shan shayi na Kolkata a Indiya.
Bayanan hoto, Shagon shan shayi na Kolkata ya zama wata gagarumar cibiya fiye da shekaru 50 da suka gabata. Ya zamo wata majalisa inda 'yan siyasa da masu fafutuka da kuma kwararru a fannoni daban-daban suke taruwa don shan shayi ko gahawa.
Maza na zaune suna hira a wani shagon shan shayi Baba Kharak Singh Marg, a birnin Delhi.
Bayanan hoto, A Delhi a kwai shagunan shan shayi na Connaught Place da Janpath duk a wani rukunin shaguna. Kuma har yanzu kungiyar masu kantunan shan shayi ta Indiya ce ke kula da su.
Wannan hoton cikin shagon sayar da shayi na Kollam ne a Indiya.
Bayanan hoto, Mista Freedman ya ce shagunan shan shayin Indiya sun yi kama da wuraren shan shayin Turai.
Ana iya ganin wani mai kura yana wucewa ta kofar shagon sayar da shayi na Kolkata a Indiya, da kuma hoton abin bautarsu Ganesha da kuma fitila a kicin din shagon shan shayi na Chennai.
Bayanan hoto, "Kana daga cikin shagon nan kana iya ganin zubar ruwan sama da hayakin taba. A takaice dai kan iya ganin abin da ke faruwa a waje daga cikin tagogin shagon," in ji Mista Freedman
Ma'aikatan shagon sayar da shayi suna hira da kyakyatawa lokacin da suke hutun rabin lokaci a ofishinsu a shagon Kottayam da ke Kerala.
Bayanan hoto, Ma'aikatan shagon sayar da shayi suna hira da kyakyatawa lokacin da suke hutun rabin lokaci a ofishinsu a shagon Kottayam da ke Kerala.
Shagon sayar da shayi na Shimla, a Indiya
Bayanan hoto, Bayan Stuart Freedman ya kammala hada hotunan shagunan sayar da shayi na Indiya, sai Dewi Lewis ya wallafa littafi a kan haka.