Yadda cutar Ebola ta fara barkewa

Cutar Ebola ta faro asali a kasar Guinea a watan Disambar bara, inda ta kama wani yaro dan shekaru biyu wanda kuma ta yi ajalinsa.

Ebola ce kuma ta kashe mahaifiyarsa da kakarsa da yarsa 'yar shekaru uku.

Daga watan Fabrairu na shekarar 2014 ne kuma cutar ta bazu zuwa wasu kauyuka uku da ke kewaye da kauyen Gekedu a kasar ta Guinea.

Cutar Ebola ta tsallaka zuwa kasashen Liberia da Saliyo wadanda ke makwabtaka da Guinea.

Kuma ya zuwa farkon watan Agustan shekarar 2014 cutar ta kashe mutane sama da 1,000 a yankin.

Yayin da kasashen yankin ciki har da Najeriya ke fadi-tashin hana bazuwar cutar, hukumar lafiya ta Duniya ta ayyana dokar ta-baci a kan cutar ta Ebola.