Hotuna: Rayuwar Kanal Gaddafi

Mo`ammar Gaddafi ya hau karagar mulkin kasar Libya ne a watan Satumban shekarar 1969, lokacin da ya jagoranci wani juyin-mulkin da ba a zubar da jini ba, inda suka hambare gwamnatin Sarki Idris.

Hotuna: Rayuwar Kanal Gaddafi
Bayanan hoto, Mo`ammar Gaddafi ya hau karagar mulkin kasar Libya ne a watan Satumban shekarar 1969, lokacin da ya jagoranci wani juyin-mulkin da ba a zubar da jini ba, inda suka hambare gwamnatin Sarki Idris.
Hotuna: Rayuwar Kanal Gaddafi
Bayanan hoto, Yana da shekaru ashirin da bakwai da haihuwa ne lokacin da akidar mulki ta shugaban kasar Masar, Gamal Abdel Nasser ta shige shi.
Hotuna: Rayuwar Kanal Gaddafi
Bayanan hoto, Gaddafi tare da Anwar Sadat na Masar da Hafez Assad na Syria da sun kafa hadaddiyar kasar Larabawa, amma ba ta yi tasiri ba.
Hotuna: Rayuwar Kanal Gaddafi
Bayanan hoto, Dabi`ar mafi yawan Shugabannin kasahen Larabawa ta rikidewa daga soja zuwa shugabannin kasa na farar-hula ta yi tasiri a kan shugaba Ghaddafi. Kuma ya fi sauran sa`o`insa dadewa a kan karaga.
Hotuna: Rayuwar Kanal Gaddafi
Bayanan hoto, Ya yi kokarin fitar da nasa salon mulki ko gwamnati a cikin kusan shekaru arba`in da daya da ya yi na mulkin kasar Libya ta hanyar tallafa wa `yan tawaye da masu ta da kayar-baya, irin su kungiyar IRA ta kasar Ireland ta arewa da Abu Sayyaf a kasar Philippines.
Hotuna: Rayuwar Kanal Gaddafi
Bayanan hoto, Yana da kyakkyawar alaka da tsohon shugaban Masar wanda aka hambarar Hosni Mubarak, kuma ance ya ji takaicin yadda aka hanbarar da Mr Mubarak din.
Hotuna: Rayuwar Kanal Gaddafi
Bayanan hoto, A wajajen karshen mulkinsa, an cire takunkumin da aka yi wa kasar Libya na mai da ita saniyar-ware sakamakon wani harin bom din da ya tarwatsa jirgin saman Pan Am a Lokerbie na kasar Scotland, a watan Disamban shekarar 1988.
Hotuna: Rayuwar Kanal Gaddafi
Bayanan hoto, Kuma janye takunkumin ya yi sanadin kwararar kasashen yamma da kamfanoni zuwa kasar domin ayyukan kwangila a fannin mai da makamashi. Ya kuma bashi damar yin tafiye-tafiye a duniya. Inda ya ke ganawa da mutane a wani tanti irin na gargajiya.
Hotuna: Rayuwar Kanal Gaddafi
Bayanan hoto, An fara rikicin da ya yi sanadin kifar da gwamnatinsa ne a watan Fabrairun shekara ta 2011 a birnin Benghazi, wanda shi ne na biyu a tsakanin manyan biranen kasar Libya.
Hotuna: Rayuwar Kanal Gaddafi
Bayanan hoto, Daga nan ne kuma dakarun Nato suka kaddamar da hare-hare a kan kasar, inda Gaddafi ya shiga buya, ya kuma rinka jawabi ga jama'ar kasar ta talabijin lokaci zuwa lokaci.
Hotuna: Rayuwar Kanal Gaddafi
Bayanan hoto, Kanal Gaddafi ya sha kai ziyara kasar Italy wacce ta yi wa Libya mulkin mallaka, kuma yana da kyakkyawar alaka da Fira Minista Silvio Berlusconi.