Zanga-zanga a Sri Lanka: 'Ba za mu bar wurin nan ba sai shugaban kasa ya sauka daga mulki'

Bayanan bidiyo, Zanga-zanga a Sri Lanka: 'Ba za mu bar wurin nan ba sai shugaban kasa ya sauka daga mulki'

Danna hoton da ke sama domin kallon bidiyon:

Shugaban Sri Lanka Gotabaya Rajapaksa ya tabbatar da cewa zai sauka daga mukaminsa.

Sai dai masu zanga-zanga da suka mamaye gidajen shugaban kasa da na firaminista sun ce ba za su bar wuraren ba sai dukkan masu rike da ragamar kasar sun ajiye mukamansu.