Bidiyon yadda fasinjoji daga Abuja ke shiga tashoshin mota don tafiya hutun Babbar Sallah
Danna hoton da ke sama domin kallon bidiyon:
A jajibarin babbar sallah a Najeriya, daruruwan fasinjoji suna ci gaba da kwarara a manyan tashoshin motocin domin yin balaguro zuwa garuruwansu.
Hakan na da nasaba da al’adar zuwa wajen iyali ko ‘yan uwa da abokan arziki domin yin bukukuwar sallah tare a gida.
Abokin aikinmu Bello Habeeb Galadanci ya ziyarci tashar mota ta Utako da ke Abuja ga kuma rahoton da ya hada mana.