Zinariya: Tsaunin da ke tsananin bukatar ababen more rayuwa a birnin Jos

Bayanan bidiyo, Zinariya: tsaunin da ke tsananin bukatar ababen more rayuwa a birnin Jos

Danna hoton da ke sama domin kallon bidiyon:

Koke-koke kan rashin ababen more rayuwa a wasu yankunan Najeriya ba sabon abu ba ne, amma labarin ya sha bamban ga al'ummar Zinariya.

Zinariya, wani karamin tsauni ne a tsakiyar Jos fadar jihar Filato, da ke tsakiyar Najeriya.

Al'ummar yankin sun shafe shekaru da dama suna rayuwa a kanshi amma ba tare da cin moriyar muhimman ababen da ake bukata domin gudanar da ingantaccen rayuwa ba.

Duk da kasancewar unguwar a tsakiyar birnin Jos, mazauna Zinariya ba su da tsaftataccen ruwan sha da asibiti da kuma hanyoyi sannan makarantar da aka gina masu ma ba ta aiki.

Wani mazaunin unguwar, Muhammad Musa Paki, ya ce hatta mata masu juna biyu da kyar suke hawa saman tsaunin saboda tudunsa da kuma rashin hanyoyi.

"Ba mu da asibiti da zai taimaka wajen jinyar mara lafiya, idan matsala ta taso sai dai mu kai su asibiti a cikin gari".

Har wa yau Muhammad ya ce "ruwan sha ma sai dai mu saya domin rijiyarmu ta burtsatsai tana kafewa da rani."