Gwara na mutu da na yi bara a kan titi in ji gurguwa mai sana'ar dinki
Danna hoton da ke sama don kallon bidiyon:
A ci gaba da kawo muku rahotanni kan masu bukata ta musamman da suka rungumi sana'o'i maimakon barace-barace a kan titi da kuma zaman kashe-wando, a yau za mu kawo muku labarin Ruth Peter wata mace gurguwa da ke sana'ar dinki a Yola fadar jihar Adamawa da ke arewa maso gabashin Najeriya.
Ruth ta bude shagonta na dinki ne a shekarar 2002 kuma ta shafe fiye da shekara 20 tana sana'ar dinki.
Duk da lalurar kafa da take da ita, matar tana dinkuna na mata da maza musamman na yayi da ake yi wa ado da duwatsun ado na mata.
Ya zuwa yanzu Ruth ta yaye dalibai da dama kuma tana koya wa sama da mata goma dinki a shagonta.
Ruth ta ce idan ta ga mai lalura yana bara sai ta ji ranta ya baci matuka.
"Idan na ga mai lafiya yana roko abun na damuna sai in ce me ya sa mai nakasa zai yi sana'a shi kuwa mai lafiya zai tsaya barace-barace?''
Ruth ta kara da cewa "da in yi bara a kan titi gwamma na mut.''