Yadda sana'ar duwatsun ado ke kawo wa guragu kudi a Jihar Kano
Danna hoton sama ku kalli bidiyo:
Sana'ar duwatsun ado na mata wato bits na daga cikin sana'o'i da mata ma su bukata ta musamman ke yi a jihar Kano dake Arewacin Najeriya.
Matan suna yin sana'ar ce domin tallafawa kansu, maimakon bara a kan tituna.
A ci gaba da kawo muku labarai na masu bukata ta musamman da su kayi fice wajen sana'o'in dogaro da kai, BBC Hausa ta gana da Safina Sani Dede wata matashiya mai sana'ar shirya bits ko kuma duwatsun ado a jihar.
Safina ta ce ta shafe shekara 15 da fara sana'ar wacce a yanzu ta ke biya mata bukatu da dama.
"Na fara wannan sana'ar daga aikatau har aka kai matakin da na kware ina sayarwa mabukata".
Matashiyar mai matakin karatun NCE, tace sana'ar ta taimaka mata wajen biyan kudin makaranta da sayan takardu da kuma sufuri yayin da take karatu.
Safina ta kara da cewa tana yin abun hannu kamar fiye da 100 da jakunkuna fiye da goma da kuma sarkar wuya da yawa a ko wane wata.
kasancewar matashiyar ta tsaya da kafafunta wajen neman na kai, ta ce bata jin dadin ganin masu bukata ta musamman su na barace-barace a kan titunan Kano da kuma sauran sassan Najeriya.
"Idan naga masu bukata ta musamman suna bara bana jindadi. Sannan ina tambayarsu dalilin da yasa basu zuwa makaranta".
Safina tace mai nakasa "shi yafi dacewa akai makaranta" fiye da wanda ba shi da ita.