Makahon malamin jami'a da ke kewar dalibansa saboda yajin aikin ASUU
Danna hoton dake sama domin kallon bidiyon:
Wani malami da ke koyarwa a Jami'ar Jihar Gombe da ke arewa maso gabashin Najeriya Ishiyaku Adamu ya ce yajin aikin da kungiyar malaman Jami'o'i a kasar ta ASUU ke yi ya jefa su cikin yanayi na kewar dalibansu.
Mallam Ishiyaku, wanda ke da larurar rashin gani, ya ce abin da ya fi burge shi shi ne kasancewa tare da dalibansa a ko da yaushe musamman idan ya tuno da yadda suke tarbarsa da kuma irin raha da suke yi kafin a fara karatu.
Ya ce tunda ba buga kwallo ko kallonta yake zuwa yi ba, dalibansa su ne manyan abokanan hirarsa.
"Gaskiya ina matukar kewar dalibaina domin da su nake hira kafin a fara karatu," in ji Mallam Ishiyaku.
A cewarsa hanyar da za ta iya yanke zaman gida da suke yi ita ce mutuntawa da kuma cika dukkan alkawura da ke tsakanin gwamnati da kuma malaman jami’oi.
Malamin ya shafe sama da shekara goma yana karantarwa duk da lalurar gani da yake da ita.
Ya ce lalurar gani ba ta yi tasiri ba wajen hana shi neman ilimi da kuma yada shi.
Tun a ranar 14 ga watan Fabrairun 2022 ne malaman jami'o'in gwamnati a Najeriya suka tsunduma cikin yajin aiki.
A halin yanzu malamai da daliban nasu sun fara kosawa da zaman gida.
Alkaluma sun nuna cewa ya zuwa shekarar 2020 Najeriya na da mutane masu bukata ta musamman sama da miliyan 27 kuma kashi biyu ne kacal na wannan adadin ya je makaranta.