Bincike: Yadda 'yan China ke samun kuɗi da tozarta yaran Afirka
Danna hoton sama ku kalli bidiyon:
A watan Fabarairun 2020 ne wani bidiyo mai kiɗimarwa ya fara karaɗe dandalin sada zumunta na China.
Wata murya da ba a gani na umartar wani rukukuni na yaran Afirka su faɗi wasu jimloli da harshen Chinanci.
Yaran na maimata kalaman cikin nishaɗi - amma ba su san cewa abin da ake faɗa musu yana nufin "ni dodo ne kuma ba na fahimta" ba. Bidiyon ya jawo ɓacin rai a China da wajen ƙasar.
Sai dai babu wanda ya taɓa ba da amsoshin: Me ya sa aka ɗauki bidiyon? A ina aka ɗauke shi? Wane ne ya ɗauke shi?
Wakilan sashen binciken ƙwaƙwaf na BBC Africa Eye, Runako Celina da Henry Mhango, sun yi balaguro har zuwa inda 'yan China ke gudanar da ayyukan tozarta yaran don samun kuɗi.