Ɗaliban da ke ceton macizai
Danna hoton da ke sama don kallon bidiyon:
Wasu ɗalibai daga Jami’ar Jahangirnagar ta Bangladesh sun ƙirƙiri wata ƙungiya don ceton macizai a faɗin ƙasar.
Ƙungiyar ta Deep Ecology and Snake Rescue na da mambobi 500 kuma sun ceci fiye da macizai 1,500 tun shekarar 2018.
Shugaban ƙungiyar Mahfuzur Rahman ya shaida wa V=BBC cewa akwai camfe-camfe sosai kan abin da ya shafi macizai da suke so su kawar da su a tsakanin mutane, ta hanyar bayar da horo.