Yadda aka koma kasuwanci a Owo bayan da zauna-gari-banza suka far wa kasuwar garin

Bayanan bidiyo, Yadda aka koma kasuwanci a Owo bayan da zauna-gari-banza suka far wa kasuwar garin

Danna hoton da ke sama domin kallon bidiyon:

‘Yan kasuwa Hausawa da ke birnin Owo na jihar Ondo sun koma bakin kasuwanci ‘yan kwanaki bayan da wasu zauna-gari-banza suka fatattake su sakamakon zargin hannu a harin da aka kai wa wata coci a karshen makon da ya gabata.

Hausawan sun ce duk da dai babu rashin rai a hare-haren da aka kai musu amma an yi musu barna.

Yanzu dai jami’an tsaro suna ta sintiri na ganin zaman lafiya ya koma.