Yadda matsananciyar yunwa ke damun yara miliyan 1.4 a Somaliya
Danna hoton da ke sama don kallon bidiyon:
Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadin cewa yara miliyan 1.4 ne suke fuskantar yunwa da tamowa a Somaliya a wannan shekarar sakamakon matsanancin fari da yankin ke fama da shi.
Yunwar ta tursasa mutum 750,000 barin muhallansu inda suka kutsa fadin ƙasar don neman abinci da ruwa da ƙasar noma.