Bidiyon Ku San Malamanku tare da Malama Habiba Yahya, matar Farfesa Maqri
Danna hoton da ke sama don kallon bidiyon:
Malama Dr Habiba Yahya Alfadarai, matar Farfesa Sheikh Ibrahim Maqari, ta ce ta yi saukar Al-Ƙur'ani mai girma tana 'yar shekara 12 da haihuwa a hannun iyayenta.
Malamar da ta yi digiri uku a harshen Larabci, ta faɗa wa BBC Hausa hakan ne cikin Shirin Ku San Malamanku da muke wallafawa duk ranar Juma'a.
An haifi Dr Habiba a unguwar Alfadarai da ke cikin birnin Zariya na Jihar Kaduna a arewacin Najeriya.
Yanzu haka malamar babbar jami'a ce a hukumar kula da ilimin Arabiyya da Musulunci ta Najeriya wato National Board for Arabic and Islamic Studies (NBAIS).