Yadda Rasha ta yi watsi da gawar sojojinta a Ukraine
Danna hoton da ke sama don kallon bidiyon:
Makonni bayan da aka kori dakarun Rasha bisa ƙoƙarinsu na ƙwace iko da babban birnin Ukraine, Kyiv, har yanzu akwai gawarwakin sojojin a yashe a Ukraine.
Al'ummar wani ƙauye na Ukraine sun binne wasu gawarwakin a inda suka gan su, wasu kuma a yanzu an tono su ana loda su a jirgin ƙasa mai firinji a ciki don mayar da su Rasha.