Yadda mummunar guguwa ta afku a Iraki sau takwas a wata ɗaya
Ku latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon:
Iraƙi na daga cikin ƙasashen duniya da suka fi fuskantar matsalar sauyin yanayi, a cewar Majalisar Dinkin Duniya.
Tun a watan Afrilu, ƙasar take gamuwa da guguwa mai ɗauke da yashin hamada, kuma dubban motane ne suka kamu da matsalar numfashi sakamakon hakan.