'Ana tsangwama ta saboda ni ƴar rawa ce kuma mai sa Hijabi'

Bayanan bidiyo, Bidiyo: Ana tsangwama ta saboda ni ƴar rawa ce kuma mai sa Hijabi

Ku latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon:

Sabrina, wata matashiya mai shekara 22 ƴar ƙasar Malaysiya kuma ƴar rawa salon K-pop ta ce tana fuskantar ƙalubale sosai daga wajen wasu mutanen da ke ganin bai dace a matsayinta na Musulma tana rawar ba.

Shekara uku da suka gabata ne ta buɗe shafi a YouTube a lokacin da ta koma Koriya ta Kudu daga garinta.

Ba ta daɗe da buɗe shafin ba ta samu mabiya fiye da 200,000, amma ta ce mu'amalar da wasu masu bibiyarta ke nunawa ba mai daɗi ba ce, musamman a matsayinta na mai saka Hijabi kuma wacce ta yi fice.