Matan da ake lalata da su kafin a ba su ruwa a Kenya

Bayanan bidiyo, Matan da ake lalata da su kafin a ba su ruwa a Kenya

Danna hoton da ke sama domin kallon bidiyon:

Nairobi, babban birnin kasar Kenya yana fama da matsalar karancin ruwa saboda wasu dalilai da suka hada da tsoffin fayif-fayif da sauyin yanayi.

Mazauna yankunan marasa galihu irin su Kibra suna samun ruwa daga 'yan ga-ruwa.

Masu sayar da ruwa suna yin tasiri sosai kan yadda ake samun ruwan a irin wadannan wurare.

Mutane suna biyan kudin ruwa da na tsaftar muhalli, sai dai hakan yana sa wa ana lalata da mata.

Masu daukar bidiyo: Njoroge Muigai, Azeezat Olaoluwa, Anne- Marie Yiannacou, Michael Onyiego