'Na gano mahaifina ta shafin Facebook bayan shekara 58 ba mu hadu ba'
Danna hoton da ke sama domin kallon bidiyon:
Wata mata a birnin Lincolnshire da ke Birtaniya ta sake haduwa da mahaifinta bayan sun yi shekara 58 da rabuwa.
Julie Lund ta wallafa sako a Facebook inda ta rika cigiyar mahaifinta kuma ta yi "matukar mamakin" irin amsoshin da aka ba ta.
Kwana hudu bayan ta wallafa sakon da ke cewa ta hadu da mahaifinta Brian Rothery, wanda ya kwashe tsawon lokaci yana rayuwa kilomita daya kacal daga inda take.