Tunkiya mai kafa biyar da aka haifa a gidan gona a Birtaniya
Ku latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon:
An haifi wata tunkiya mai ƙafa biyar a wani katafaren gidan gona a Ingila.
Wannan lamari ya zama wani abin al'ajabi da ba kasafai ake gani ba.
Tunkiyar na cikin halin lafiya kamar yadda likitocin dabbobi suka ce.