Likita ɗan Najeriya da ke taimaka wa baƙaƙen fata a kan iyakar Ukraine

Bayanan bidiyo, Likita ɗan Najeriya da ke taimaka wa baƙaƙen fata a kan iyakar Ukraine

Ku latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon:

Wani likita ɗan Najeriya da ya tsere daga Ukraine ya ce hankalinsa ba zai kwanta ba sai ya tsaya ya dinga taimaka wa baƙaƙen fata ƴan uwansa da ke cikin buƙatar taimako a kan iyaka.

Ya bar Ukraine ne saboda yaƙin da ake yi kuma ya naɗi bulaguronsa daga ƙsar zuwa Poland a bidiyo.

Dr Awofaa Gogo-Abite ya shafe shekara 14 a Ukraine kuma yana aiki ne a matsayin likitan fiɗa kuma malamin jami’a.