Yadda ƴan Sri Lanka suka yi makokin mutuwar giwa mai shekara 69
Ku latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon:
Ƴan Sri Lanka sun yi ta zaman makokin wata giwa da suke ji da ita a ƙasar wacce ta mutu tana da shekara 69.
An sanya gawar giwar a akwatin gwal.
Giwar mai suna Nadungamuwa Rajaita ce mafi muhimmanci a cikin giwaye 100 da ake amfani da su wajen bukukuwan addinai na ƙasar.