Mata da mijin da suke tare tsawon shekara 91 ba saki ba yaji
Ku latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon:
Zechariah da Shama’a suna tare tsawon shekara 91 a yin aurensu.
A matsayin su na marayun Yahudawa a Yemen, sun yi aure suna da ƙarancin shekaru don guje wa yi musu aure ba bisa tsarin addini da al'adarsu ba.
Sun fuskanci talauci da cin zarafi, kuma suna cikin Yahudawan Yemen na farko-farko da suka koma Isra'ila bayan samar da ƙasar.