Africa Eye Kush: Yadda tabar wiwi take haukata matasa a Sierra Leone
Latsa hoton da ke sama domin kallon bidiyon:
Wani sabon nau'i na wiwi ya karade kasar Sierra Leone a watanni 18 da suka wuce, lamarin da ke da mummunan sakamako.
Ana kiran wannan wiwin da suna Kush – sai dai a fadin duniya an fi saninta da K2 ko Spice.
Tyson Conteh ya bi diddigin wannan batu a Freetown, babban birnin kasar kamar yadda za ku gani a shirin BBC Africa Eye.