Kalli jirgin saman da ya yi hatsari a kan titin jirgin kasa
Ku latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon:
Ƴan sanda a Los Angeles na Amurka sun janye wani matuƙin jirgi da jirgin samansa ya yi hatsari a kan titin jirgin ƙasa, ƴan mintuna kaɗan kafin jirgin ƙsan ya biyo hanyar.
Wani mazaunin yankin da abin ya faru ya ɗauki hoton yadda ya kasance a wayarsa.
A yanzu dai matuƙin jirgin na asibiti kuma yana samun kulawa.