Yakin Tigray: Jaririn da mahaifiyarsa ba ta da ruwan nonon da za ta ba shi saboda bala'in yunwa
Latsa hoton da ke sama domin kallon bidiyon:
Wani asibiti da ke yankin Tigray mai fama da yaki na kasar Ethiopia ya yi gargadin cewa abincin da yake bai wa yara masu fama da tamowa ya kare.
Ma'aikatan lafiya sun mika rahoto ga kungiyoyin agaji inda suke neman taimako.
Asibitin Ayder Referral Hospital ya ce ba shi da isassun kayan aikin da zai kula da lafiyar wani jariri dan wata uku Surafael, wanda mahaifiyarsa ta kai shi asibitin a kanjame sakamakon tamowa.