Garin da mata ne kawai suke sarauta a arewacin Najeriya
Latsa bidiyon da ke sama domin kallon bidiyon:
Shin kun taba sanin cewa akwai wata masarauta da mata zalla ke mulki a arewacin Najeriya?
Masarautar Dingep da ke karamar hukumar Ganye a jihar Adamawa a arewa maso gabashin kasar ta shafe sama da karni 7 karkashin jagorancin mata, wani abu da ya sha bambam da sauran masarautu da ke arewacin kasar.
Garin yana da yawan jama'a sama da mutum dari biyar kuma sarauniya ce ke gudanar da dukkan aikace-aikace da sarakunan gargajiya maza ke yi a wasu masarautun.