Jirage marasa matuka da ke maye gurbin likitoci a Cape Verde
Latsa hoton da ke sama domin kallon bidiyon:
Masanin kimiyyar kwamfuta Erico Pinheiro ya kera jirgi mara matuki domin kai magunguna zuwa yankunan karkara da ke kasarsa da ke tsiribin Cape Verde.
Tuni wannan jirgi ya ceto rayukan mutane da dama kuma yana isa kananan tsibirai kuma masu nisa - wuraren da ake kwashe kwanaki da dama kafin masu kula da lafiya su isa.