Yadda China ke sauya Hong Kong 'har abada'

Bayanan bidiyo, Bidiyo: Yadda China ke sauya Hong Kong 'har abada'

Ku latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon:

A hankali a hankali China na ta zame wa Hong Kong ƴancinta ta hanyar amfani da wata Dokar Tsaro ta Ƙasa da kuma Dokar zaɓe ta masu kishin ƙasa.

Gabanin zaɓukan dokokin da za a yi ranar Lahadi 19 ga watan Disamba, a kuma lokacin da ake yanke wa mutane da dama hukunci ƙarƙashin sabbin dokoki, mun duba dalilan da suka yadda ake kallon Hong Kong a idon duniya za su sauya har abada.