Abin da ya sa na kirkiro manhajar kallon fina-fina Hausa

Bayanan bidiyo, Abinda yasa na kirkiro manhajar kallon fina-fina Hausa

Ku latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon:

Hajiya Maijidda Shehu Modibbo ta kirkiri wata manhaja da ke dauke da fina-fina da wakokin Hausa da ake kira Kallo.

Ta ce makasudin da yasa ta kirkiri manhajar shi ne shigowan fasaha da ya sa kowa na dauke da waya, babu masu amfani da cd ko kaset.

Ta kara da cewa akwa ma'abotan kallon fina-finan Hausa da dama a fadin duniya, hakan ya sa ta yi tunanin fara wannan dandali.