Gwamnonin Najeriya ba sa tsoron zaben 'yar tinke - Badaru

Bayanan bidiyo, Gwamnonin Najeriya ba sa tsoron zaben 'yar tinke - Badaru

Latsa bidiyon da ke sama domin kallon bidiyon:

Gwamnan Jigawa da ke arewacin Najeriya Muhammadu Badaru Abubakar ya ce gwamnonin jihohin kasar ba sa jin tsoron gudanar da zaben cikin gida ta hanyar 'yar tinke ko kato-bayan-kato.

Gwamnan ya shaida wa BBC cewa gwamnonin kasar ba sa adawa da gudanar da zabe ta hanyar 'yar tinke, yana mai cewa tsadar gudanar da shi ne abu da suke so a fahimta.

Ya kara da cewa ita kanta hukumar zaben kasar za ta sha wahala wajen gudanar da shi baya ga daukar lokaci da kuma tsadar da ke cikinsa.