Iyakar Belarus-Poland: 'Mun gwammace mu mutu a nan, da mu koma kasarmu'

Bayanan bidiyo, 'Mun gwammance mu mutu a nan, da mu koma kasarmu'

Latsa hoton da ke sama domin kallon bidiyon:

Dakarun Poland sun hana daruruwan mutane tsallaka iyaka daga Belarus, inda 'yan ci-ranin da suka kagu suke tattara itatuwa domin gina gidaje a yayin da ake matukar sanyi.

Tarayyar Turai ta ce za ta kara sanya takunkumi kan Belarus da kuma mutanen da ke kusa da shugabanta a matsayin wani martani kan rikicin da suka haddasa na 'yan ci-rani.

Tarayyar Turai ta zargi Belarus da tura 'yan ci-ranin zuwa kan iyakar da ke gabashi da zummar kassara tsaron yankin, zargin da Belarus ta musanta.