Taraba: Yadda satar mutane ta zama ruwan dare a Jalingo
Ku latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon:
Mazauna Jalingo a jihar Taraba da ke arewa maso gabashin Najeriya na kokawa kan karuwar satar mutane a kwaryar birnin da kuma wasu sassan jihar.
Lamarin ya fi kamari ne a unguwannin da ke bayan gari inda kusan kowa ka iya fadawa tarkon masu garkuwa da mutanen.
Ko da yake rundunar 'yan sanda a Taraban ta ce ta bullo da sabbin matakai domin magance matsalar, amma hakan bai kauda tsoro da masu satar mutanen suka dasa a zukatan al'umma ba.
Satar mutane domin karban kudin fansa ba sabon abu ba ne a jihar Taraba, amma matsalar ta kara ba da tsoro ne a 'yan kwanakinnan inda mutane ke bacewa bat ba tare da jin duriyarsu ba.
Wannan dalilin ne yasa da zarar duhu ya fara gabatowa sai ka ga sawu ya dauke a yankunan da ke wajen gari.
A wannan bidiyon mun yi hira da wani da ke da gida a irin unguwannin nan na bayan gari wanda ya sha da kyar daga hannun masu garkuwa da mutanekuma yace sau da dama da 'yan gari ake hada baki wajen satar mutane.
Irin wadannan labaran masu sosa rai ne dai ke kada hantar mazauna Jalingo duk da cewa suna fadar gwamnati.
Ko da yake a duk lokacin da aka kai irin wadannan koke-koke ga jami'an tsaro martani da suke bayarwa kusan koda yaushe shi ne na yin iya kokarinsu wajen digawa matsalar aya.
Amma a wannan karon jami'in hulda da jama'a na rundunar 'yan sanda a jihar ta Taraba DSP Abdullahi Usman yace rundunar ta tsaurara atisaye da kuma tattaunawa da shugabannin al'umma a dukkan bagarori domin shawo kan matsalar.
Wata alamar dake nuna babu wanda zai bugi kirjin cewa yafi karfin shiga hannun masu garkuwa da mutane a Taraba itace yadda masu ido da kwalli da kuma 'yan rabbana ka wadata mu ke shiga hannun barayin.
Ko a karshen shekarar 2020 sai da aka sace wani dan majalisar dokokin jihar Taraba.
Sannan a cikin 'yan shekarunnan an yi garkuwa da fitattun mutane kamar mahaifiyar mataimakin gwamnan jihar da tsohon mai magana da yawun gwamnan jihar da dai sauransu.
A yayin da wannan matsalar ta satar mutane ke kara yawaita a sassa daban-daban na Najeriya, fatan al'umma shi ne ganin karshenta da kuma samun zaman lafiya mai dorewa.