Sheikh Aminu Daurawa: Abin da ya sa na ƙirƙiri manhajar hada aure da ilmantar da ma’aurata
Latsa hoton sama domin kallon bidiyon:
Fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Aminu Daurawa ya ƙaddamar da wata sabuwar manhaja ta haɗa aure da ba ma’aurata shawara wadda ya kira “Auratayya.”
Ya ce auren zawarawa sama da 10,000 da suka haɗa a jihohin Kano da Sokoto da kaduna da katsina da Gombe ne ya sa suka ga akwai bukatar a fadada ilmantar da ma’aurata.
“Babban matsalar aure shi ne rashin bincike da rashin cikakken ilimi ga rayuwar auren” in ji Malamin.
Ya ce manhajar ta ƙunshi ɓangarori da suka shafi masu neman aure da masu neman shawarwarin aure da kuma masu fuskantar matsalolin aure.