Addinan da suka fara amfani da mutum-mutumi a matsayin mai wa'azi
Ku latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon:
Basirar na'ura wato AI na sauya yadda muke yin abubuwa da dama kamar su abinci da kiwon lafiya da tafiye-tafiye har ma addini.
Ƙwararru sun ce manyan addinan duniya a yanzu suna tattauna alaƙarsu da Artificial Intelligence AI, kuma wasu sun fara sanya yanayin ibada a cikin wannan fasahar.
Malaman addini na mutum-mutumi za su iya yin addu'a su yi jana'iza har ma da lallashin waɗanda ke cikin damuwa ta hanyar addu'a.
A wannan bidiyon, mun yi duba kan ko alaƙar AI da addini na da tasiri, ko kuma zai iya sauya yanayin yadda mutane ke yin ibada.