Mauritania: Garin da ake bai wa dabbobi kwalaye su ci saboda rashin abinci
Latsa lambar da ke sama don kallon bidiyo:
A arewacin Mauritania, mutane na ganin tasirin sauyin yanayi.
Ɗumamar yanayi da gusowar hamada na korarar al'ummomi kuma kamar yadda jerin rahotanni na Rayuwa a digiri 50 a ma'aunin Celcius ya gano, mutane da yawa na barin gidajensu na gado don neman rayuwa mai inganci.