Yadda daukewar Facebook da WhatsApp da Instagram ya shafi ƴan Najeriya

Bayanan bidiyo, Yadda daukewar Facebook da WhatsApp da Instagram ya shafi ƴan Najeriya

Latsa hoton sama domin kallon bidiyon

Shafukan sada zumunta da muhawara na Facebook da WhatsApp da Instagram sun dawo aiki bayan matsalar daukewa da aka samu wadda ta kai tsawon kusan sa'a shida in ji kamfanin Facebook.

Kamfanin ya dora alhakin matsalar a kan wata tangarda daga wurinsu.

An kasa samun dukkanin shafukan uku mallakin Facebook a kan wayoyin hannu da intanet.

Lamarin ya shafi manyan kasahen duniya da ma masu tasowa ciki har da Najeriya

Wasu masu amfani da shafukan na Facebook da WhatsApp da kuma Instagram a kasashe da dama sun shiga rudani bayan da suka fara ganin matsalar. Wasu sun dauka wayarsu ce ta samu matsala yayin da wasu suka dauka kudin intanet dinsu ne (wato data) ya kare.

Masu amfani da shafukan a Najeriya sun bayyana yadda katsewar Facebook, Instagram da kuma WhatsApp ya shafe su