Ana ce-ce-ku-ce kan aikin gadar sama a jihar Taraba

Bayanan bidiyo, Ana ce-ce-ku-ce kan aikin gadar sama a jihar Taraba

Latsa hoton sama domin kallon bidiyon rahoton

Gwamnatin jihar Taraba da ke arewa maso gabashin Najeriya da kuma bangaren jam’iyyar adawa ta APC a jihar na ce-ce-ku-ce kan aikin gadar sama da gwamna Darius Ishaku ya ƙaddamar a shekarar 2020.

Gwamnatin Darius ta ware naira biliyan 34 domin gudanar da aikin gadar da kuma faɗaɗa manyan tituna biyu da suka bi kanta.

A yayin da gwamnatin jihar ke cewa tana aikin ne domin rage cinkoso, ita kuwa jam’iyar hamayya ta APC ta ce akwai ayyukan titunan karkara da suka fi muhimmanci gwamnati ta mayar da hankali kansu maimakon gadar sama.