Ina jin takaicin yadda ake sakin masu laifi idan an kama su — Sarkin Zazzau

Bayanan bidiyo, Ina jin takaicin yadda ake sakin masu laifi idan an kama su — Sarkin Zazzau

Ku latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon:

Sarkin Zazzau Ambassador Ahmad Nuhu Bamalli, ya koka kan yadda ake sakin wasu ɓata-gari da ake zargin su da hannu a sace sacen jama'a da kuma wasu laifuffuka.

A wata hira da BBC Hausa, Sarkin wanda a cikin mako mai kamawa ne zai cika shekara daya a kan karagar sarauta, ya ce wajibi ne sai an dukufa wajen gudanar da addu'o'i don shawo kan matsalar tsaro da ta addabi Najeriya.