Labarin yaron da kura ta cirewa ido daya da hanci da lebe a Zimbabwe
Ku latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon:
Wani yaro dan kasar Zimbabwe dan shekara tara mai suna Rodwell Nkomazana ya rasa ido daya da rabin hancinsa da leben sama a lokacin da kura ta kai masa hari.
Ya tafi kasar Afirka Ta Kudu don wata tawagar likitoci ta yi masa tiyata kyauta.
A can din ya hadu da wasu matasa biyu da suka taba samun kansu a irin wannan halin.