Taliban ta dawo - ko al-Qaeda za ta mara mata baya?

Bayanan bidiyo, Taliban ta dawo - ko al-Qaeda za ta mara mata baya?

Ku latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon:

Bayan kai hare-haren 9 ga watan Satumban 2001, Amurka ta fara farautar kungiytar al-Qaeda a cikin duwatsu da tsaunukan Afghanistan, kungiya mai ikirarin jihadin da ta zamo ta ta'addancin da ta mamaye kanun labarai.

A shekara 20 din da suka biyo bayan hakan, al-Qaeda ta kai wasu munanan hare-haren a wurare daban-daban a fadin duniya.

Amma ina labarin kungiyar ne a yanzu, shin barazanar ta'addancinta na iya sake dawowa a yanzu?

Murad Batal Shishani na shashen BBC Arabic ya yi bayanin hakan.