Makarantar da ake koyar da ilimin fasahar zamani da harshen Hausa a Kano

Bayanan bidiyo, Makarantar Engausa ta Kano

Ku latsa alamar hoton da ke sama domin kallon bidiyon makarantar Engausa

Matasa a arewacin Najeriya sun fara gano cewa matsalar harshe ce ke janyo koma-bayan ‘yan uwansu matasa musamman a fagen ilimin kimiyya da fasaha.

Wato da dama dalibai ba sa fahimtar hakikanin darussan da ke kunshe a cikin abubuwan da ake koya musu tun daga matakin firamare har zuwa makarantun gaba da sakandire sakamakon rashin fahimtar harshen Turanci wanda da shi ake koyarwa.

Hakan ne ya sa wani matashi a Kano, Injiniya Mustapha Habu ya bude wani aji da ake kira da Engausa domin koyar da matasa harkokin fasahar zamani a cikin harshen Hausa da Turanci.

Injiniya Habu dai ya ce “duk kasashen da a yau suka ci gaba to za ka gani suna amfani da harshensu ne a saboda haka mu ma muka ga bukatar hakan”.

Kawo yanzu dai wannan makaranta ta yaye dalibai fiye da 500, inda kusan dukkansu kodai suna tsaye da kakafunsu ko kuma an dauke su ayyuka a kamfanoni daban-daban.

"Muna daukar har wadanda ba su je makaranta ba kai har ma da almajirai kuma ka ga sun zama zakakurai. Kuma wani abu da muke yi shi ne bayan sun kammala Engausa ba wai kawai za mu kyale su su tafi shi kenan ba.

Muna shirya musu wani kwarya-kwaryar koyarwa a scoshiyal midiya a duk ranar Juma'a. Ta haka ne muke sanin halin da suke ciki," in ji Injiniya Mustapha Habu.

A kullum Engausa na zakulo matasa fasihai daga ko'ina a arewacin Najeriya domin tallafa musu su tsaya da kafafunsu.

Za a iya cewa wannan ce makaranta irinta ta farko a arewacin Najeriya wadda matashi zai je ya lakanci wata sana'a ta zamani ko da kuwa bai je makarantar boko ba.