Afghanistan: Yadda aka yi yamutsi a filin jirgin saman Kabul yayin da 'yan kasar suke son tserewa daga mulkin Taliban

Bayanan bidiyo, Yadda aka yi yamutsi a filin jirgin saman Kabul yayin da 'yan Afghanistan suke son tserewa

Wani bidiyo ya nuna dubban 'yan Afghanistan a filin jirgin saman Kabul suna kokarin tserewa daga kasar yayin da kungiyar Taliban ta kwace iko da babban birnin.

An ji karar harbe-harbe ranar Litinin, kuma ganau sun shaida wa BBC cewa an kashe fararen hula.

Rahotanni sun ce dakarun Amurka sun yi harbi a iska da zummar tarwatsa dandazon jama'ar da ke yunkurin shiga jirgin kasar.

Kungiyar Taliban ta kwace iko da kasar, kusan shekaru 20 bayan wata gamayyar dakarun tsaro da Amurka ta jagoranta ta kore su daga mulki.